Zan bi umarnin kotu na dawo da kudi — Zuma

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Zuma ya ce bai yi wannan abu da niyya ba

<span >Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya yi alkawarin bin umarnin kotu na dawo da kudaden gwamnati da ya yi amfani da su wajen gina gidansa na kashin kansa.

A wani jawabi da ya gabatar kasi tsaye a talbijin, Mista Zuma ya ce, ''Ina girmama doka kuma zan yi yadda aka umarce ni.''

Shugaba Zuma ya godewa kotun bisa hukuncinta ya kuma ce dama ya sha nana cewa zai dawo da wadannan kudade.

Koyun ta ce Mista Zuma ya ki martaba kundin tsarin mulkin kasar.