AMAA: An karrama Tijjani Ibrahim

Hakkin mallakar hoto Saleem Tijjani Ibrahim Facebook
Image caption Saleem Tijjani Ibrahim da mahaifiyarsa a bikin, a inda aka karrama marigayin.

Marigayi Tijjani Ibrahim na daya daga cikin wadanda aka karrama a bikin raba kyautuka na AMMA Awards na wannan shekara.

AMAA Awards shi ne bikin karrama mawaka da masu shirya fina-finai na Arewa, kuma marigayi Tijjani Ibrahim na daya daga cikin fitattun masu bayar da umarni a Kannywood.

An gudanar da bikin rarraba kyautukan na AMAA ne a ranar Asabar a jihar Kano, Najeriya a inda ya samu halartar Minstan kula da harkokin matasa da wasanni Mista Solomon Dalong da kuma sauran manyan baki daga ciki da kuma wajen kasar.