Matatar mai ta Kaduna za ta soma aiki

Hakkin mallakar hoto

Sashen man petur na gwamnatin Nigeria ya ce, cikin mako biyu nan gaba matatar mai ta Kaduna za ta soma aiki.

Wannan mataki na da nufin ganin an kawo karshen matsalar karancin mai da 'yan Nigeria ke fuskanta..

A wata ziyara da suka kai matatar mai ta Kaduna masu fada a ji a harkar mai sun ce, da zarar an samu danyen mai daga Warri matatar Kaduna za ta soma aiki.

Wasu na danganta matsalar mai da ake fama da ita a Nigeria ga matsalolin da suka dabaibaye matatun mai na Kaduna, da Fatakwal da Warri.

Tun daga watan Janairu ne dai matatar mai ta Kaduna ta daina aiki sanadiyyar rashin samun danyen mai.

Koda a cikin mako mai ƙarewa ministan mai Ibe Kachukwu ya sanar da wani tsari da zai baiwa kwararru damar gudanar da matatun mai na Nigeria.

Matsalar karancin mai kusan za a iya cewa, ta ki ci, ta ki cinyewa a Nigeria.