Mahamadou Issoufou ya fara sabon wa'adi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Issoufou ya lashi takobin yaki da ta'addanci

A Jamhuriyar Niger an rantsar da shugaba Muhammadou Issoufou karo na biyu bayan lashe zaben da aka yi a watan da Fabrairu da ya wuce.

Cikin makon jiya ne hukumar zabe CENI ce ta bayyana shugaba Muhammadou Issoufou a matsayin wanda ya lashe zaben kasar.

Sai dai gamayyar jam'iyyun adawa dake goyon bayan Hama Amadou sun yi watsi da zaben da ya baiwa shugaba Issoufou nasara.

Wannan zai kasance wa'adin mulki na biyu kenan da shugaba Issoufou zai yi.

Ana sa ran shugabannin kasashe za su halarci bikin rantsarwar.

Tuni shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya aike da wasikar taya murna ga shugaba Issoufou.

Shugaba Buhari ya yi masa fatan alheri, sai dai ya nuna damuwa na yadda ba zai samu damar halartar bikin ba saboda taron Makamashin Nukiliya da yake halarta a birnin Washington na Amurka.