Najeriya ta kudiri aniyar bunkasa Noma

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar rage dumbin kudaden da ake kashewa wajen shigo da abinci daga waje.

A wata ganawa da Firaministan Denmark Mr Lars Rasmussen a Washington, shugaba Buhari ya sake jaddada cewa kudirin gwamnatinsa na fadada hanyoyin inganta tattalin arzikin kasar.

Yace kasar na da dumbin albarkatun gona da ma'adinai saboda haka za'a yi cikakken amfani da wannnan domin rage rashin ayyuka da kuma ciyar da kasar gaba.

Shugaban yace kasar na maraba da masu zuba jari a fannin ayyukan noma da ma'adinai daga kasashen da suka kware sosai a wadannan fannoni guda biyu wadanda yace a baya Najeriya ta yi watsi da su saboda samun albarkatun mai, amma yanzu ya zama wajibi a koma gare su.

Haka kuma shugaba Buhari ya nanata kudirin gwamnatinsa na hada hannu da sauran kasashe domin inganta tsaro a kan tekun Guinea.