Matsalar mutuwar mata wajen haihuwa.

Najeriya na daya daga cikin kasashe masu tasowa da ke fama da matsalar mutuwar mata a sanadiyar haihuwa.

Wanan lamarin kan sanya wasu hukumomi da kungiyoyi masu bayar da agaji na duniya zuwa kasar domin bayar da taimakonsu wajen rage wannan matsala.

A irin hakan ne kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya ta, Medecins Sans Frontieres, MSF, wato Doctors Without Borders,ke ta kokarin a wanan fani.

A yanzu haka dai kungiyar ta MSF ta tsawaita yarjejeniyar aikinta da kuma fadada shi a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya.

Wanan kuma da fatan rage yawan mutuwar mata a sanadiyyar haihuwa.