An kashe mutane 30 a Nagorno-Karabakh

Hakkin mallakar hoto Getty

Faɗa mafi muni cikin shekaru 20 da suka gabata ya ɓarke Nagorno-Karabakh da ake taƙaddama akansa.

Faɗan yayi sanadiyyar mutuwar mutane aƙalla 30.

Rahotanni sun ce, anyi amfani da manyan makamai a fadan tsakanin dakarun Azerbaijan da na Armenia.

Dukka ɓangarorin biyu suna dorawa juna alhakin barkewar fadan.

Ƙasashen duniya sun soma kiran a tsagaita wuta.

Nagorno-Karabakh dai yanki ne dake Azerbaijan, amma yana karkashin ikon Armeniyawa 'yan aware tun bayan fadan da aka kawo karshensa a 1994.