Brussels:Jiragen sama sun ci gaba da tashi

Hakkin mallakar hoto Reuters

Jirage sun ci gaba da tashi daga filin jiragen sama na Brussels kwanaki goma sha biyu bayan harin kunar bakin wake da aka kai filin jirgin wanda ya hallaka mutane goma sha shida.

Gabanin tashin wani jirgi mallakar Brussels, sai da shugaban hukumar filin jirgin saman na Zaventem Arnaud Feist ya sanar da hakan ga taron yan jarida yayinda jama'a suka rika tafi da jin labarin.

Yana mai cewakan mu a hade yake tsintsiya madaurinki daya, mun dawo.

Jirage uku ne kacal aka tsara za su tashi a yau lahadi, an kuma tsaurara tsaro da tsananta binciken motoci masu shiga filin jirgin saman.

Hukumar filin jirgin saman ta ce harkoki ba za su kankama sosai ba har sai nan da karshen watan Yuni.