Jami'in FIFA ya shiga hannu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabon shugaban FIFA Gianni Infantino ya sha alwashin magance cin hanci da rashawa a hukumar

Hukumar kwallon kafar ta duniya FIFA ta soma binciken wani babban dan kwamitin da'a na hukumar bisa zargin alaka da wani tsohon mataimakin shugaban hukumar wanda aka tsare shi a watan Mayun shekarar 2015.

Ana binciken Mista Juan Pedro Damain lauya, kuma dan a kasar Uruguay da alaka da Eugenio Figuredo tsohon shugaban hukumar a wani bangare na binciken da Amurka ke yi na cin hanci da rashawa a wasan kwallo kafa.

Takaradun sirrin da aka tsegunta na nuna cewa Mista Damian da kamfaninsa na lauyoyi sun taimaka wa a kalla kafanonin bakwai zuba jari a ketare da ke da alaka da Mista Figuredo.

Wanda ake zargi Mista Damian, ya ki ya ce komai game lamarin, wasu takardun sirri da aka kwarmata ya alakanta wasu shugabanin kasar Panama da gamin bakin wasu kamfanin lauyoyi halarta kudin haram da kuma kaucewa biyan haraji.

Makonni shida ke nan da soma aikin sabon shugaban FIFA Gianni Infantino, wanda ya sha alwashin kawo gyara a hukumar sai ga shi wannan abin kunyar ya faru.