Za mu hanzarta ci gaban Najeriya —Buhari

Hakkin mallakar hoto State House

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi iya kokarinta wajen kawo cigaba cikin sauri a kasar.

Shugaba Buhari ya bayanawa 'yan Najeriya mazauna kasashen waje a ziyarar da ya kai Amurka.

Ya ce gwamnatinsa nada aniyar ganin cewa ta gyra kura- kuran da aka yi a can baya wadanda ke janyo wa kasar cikas.

Shugaba Buhari ya sake alkawarin samar da ababen more rayuwa a cikin kasar.

Ya kuma ce gwamnatinsa za ta cigaba da tuntubar 'yan kasar da ke zama a kasashen waje akan gudumuwar da za su bayar ga cigaban kasarsu.

Karin bayani