Amfani da Wi-fi kyauta a filayen wasa a Burtaniya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Koda ya ke ba za'a bada damar bude daukacin shafuffukan Internet ba ta wannan hanya.

Hukumar shirya wasannin League a Burtaniya ta sanar da cewa za'a fara amfani da Internet ta hanyar Wifi kyauta a filayen da ake buga wasannin Championship da League One da kuma League Two.

Masu kallon kwallon kafa za su iya samu labarai da kuma bayanai na caca da ake yi a hanyoyin sada zumunta ta wata manhaja ta musamman.

Koda ya ke ba za'a bada damar bude daukacin shafuffukan Internet ba ta wannan hanya.

Hukumar ta ce a halin yanzu kusan daukacin kungiyoyi kwallon kafa sun rattaba hannu a yarjejeniyar da cimma don samar da Wifi kyauta a filayen da ake buga wasannin.