Erdogan:Ban ji dadin kalaman Obama ba

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yace kalaman da Obama ya yi game da tauye yancin kafofin yada labarai a Turkiyya sun bata masa rai.

Shugabannin biyu sun gana a makon da ya gabata a daura da taron koli kan makamashin nukiliya.

Sai dai yace basu tattauna batun yancin yan jarida ba kuma bai ji dadin cewa Obama ya yi magana kan batun a bayan idonsa ba.

A ranar Juma'a Mr Obama yace matakan da Turkiyya ke dauka kan kafofin yada labarai abin damuwa ne kwarai, yace ya baiyana ra'ayinsa kai tsaye ga Mr Eedogan