Chad: Kungiyoyin fararen hula sun janye daga hukumar zabe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Idris Deby na son yin tazarce karo na biyar
Har a yanzu al'amura sun kasa daidaita a kasar Chadi kasa da mako guda bayan da aka gudanar da zabe a kasar.

A yanzu haka kungiyoyin fararen hula sun bayyana janyewarsu daga cikin harkokin hukumar shirya zabe mai zaman kanta ta kasar.

Kungiyoyin sun kuma jaddada cewa za su yi wani gangami na lumana a ranar Talata.

A wani bangare kuma kotu a kasar Chadi ta tsaiyar da ranar 7 ga watan Afrilu domin sauraron shari'ar da ake yi wa wasu jigogin kungiyoyin fararen hula su hudu, da aka tsare bisa ga zarginsu da tayar da zaune tsaye da kuma bijire wa hukuma.