Ana ci gaba da takaddama kan zaben Chadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Chadi Idriss Deby

Rahotanni daga kasar Chadi sun ce ana ci gaba da takaddama tsakanin kungiyoyin farar hula da gwamnatin kasar game da tsayawa takara da Shugaban kasa da Idriss Deby ya yi.

A ranar Litini ne dai jami'an 'yan sanda suka sake tsare wani shugaban kungiyar fararen hula, Dokta Albissaty Saleh Allazam wanda shine na mutum na 5 da yake hannun hukumomin tsaro a halin yanzu.

Ana dai zargin mutane ne da yunkurin ta da zaune tsaye da kuma rashin mutunta dokar kasa.

Sai dai kuma kungiyoyin farar hular sun dage cewa za su fito ranar Talata domin yin gangami na lumana.