Djibouti ta kori BBC kafin zabe

Image caption Shugaban Djibouti, Isma'il Omar Guelleh

Kasar Djibouti ta kori 'yan jaridar BBC gab da fara zaben kasar na ranar 8 ga watan Afrilu.

Kafin dai a kori 'yan jaridar, sai da aka kulle su har na tsawon awanni 16, bayan da suka yi hira da ministan harkokin wajen kasar da dan takarar jam'iyyar adawa.

'Yan jaridar wadanda suka hada da wakilin BBC kan tsaro a nahiyar Afirka, Tomi Oladipo, sun sami tantancewa kafin ma su shiga kasar.

Tuni kafar yada labarai ta BBC ta rubutawa gwamnatin kasar takarda kan sanin dalilin korar 'yan jaridar nata.

Image caption Ranar 8 ga watan Afrilu ne 'yan kasar za su kada kuri'ar zaben shugaban kasa.

Har yanzu dai gwamnatin ta Djibouti ba ta ce komai ba.

Sai dai kuma kungiyar 'yan jaridu ta duniya ta ce Djibouti tana da tarihin cin zarafin 'yan jarida.

Kungiyar ta sanya kasar a matsayi na 170, a kasashe 180 masu dakile 'yancin samun bayanai.

Shugaban Djibouti, Ismail Omar Guelleh yana tsaya takara domin neman shugabancin kasar karo na hudu