'Za mu kawo karshen satar mutane a Kaduna'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomi sun ce ana daukan matakai na hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro don magance matsalar

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta dukufa wajen magance matsalar tsaron da ake fama da ita a jahar Kaduna, musamman sace sacen jama'a ana garkuwa da su don neman kudin fansa.

Tuni dai babban sipeton 'yan sanda Najeriyar Solomon Arase ya umurci mataimakin shugaban 'yan sanda AIG na shiyya ta 7 AIG Ballah Nasarawa da ya koma Kaduna har sai al'amurran tsaro sun inganta a jihar.

A 'yan kwanakin nan matsalar fashi da makami da kuma sacen mutane ana garkuwa da su na ci gaba da ta'azzara a jahar musamman a kananan hukumomin Jere da Kagarko da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A kwanakin baya ne wa su al'ummomin kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari a jihar Kaduna suka koka da sabon salon fashi da makami da garkuwa da mutane da kashe-kashe a yankunan su.

A cikin wata takarda da suka aikewa gwamnan jihar Kaduna, al'ummomin sun bukaci gwamnati da ta kara kaimi don kawar da bata garin da suka addabi al'umma.

Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta na sane da matsalar kuma ana daukan matakai na hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro don magance matsalar.