Wadanda suka sha fama da Ebola na zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kimanin mutane dubu 11 ne Ebola ta hallaka a kasashe uku na yammacin Afrika
Mutanen da suka rayu bayan sun sha fama da cutar Ebola a Saliyo suna zanga-zanga a duk fadin kasar kan abin da suka kira rashin kulawar gwamnati.

Sun ce wadansu mutanen sun mutu ne sakamakon cutar saboda rashin samun kulawar lafiya daga gwamnayi.

Matan da suka rasa mazajensu sakamakon cutar sun ce gwamnati ta gaza wajen cika alkawarin da ta yi musu na basu tallafi, wanda hakan ke nufin 'ya'yansu ba za su iya komawa makaranta ba.

Har yanzu dau hukumomi basu ce komai kan wannan batu ba.