Za a samar da fasfo na bai daya a Afrika

Hakkin mallakar hoto
Image caption Nkosazana Dlamini Zuma ce shugabar kungiyar tarayyar Afrika

Shugabannin kasashen Afrika za su fara amfani da fasfo iri guda na nahiyar daga watan Yulin wannan shekarar.

Hakan dai wani yunkuri ne na samar da takardun bai daya a nahiyar da kungiyar Afrika ke yi.

Shugabar kungiyar tarayyar, Dlamini Zuma ce ta bayyana hakan a Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Shugabar ta ce samar da fasfo na bai daya zai taimaka wajen bude iyakokin kasashe a nahiyar ta yadda mutane za su yi zirga-zirgar ba tare da wani kaidi ba.

Inda ta kara da cewa hakan kuma zai gaggauta dunkule nahiyar waje guda.

Dlamini ta ce matakin ya biyo bayan shawarar shugabannin kasashen suka bayar, inda suka amince da bayar da visa kwanaki 30 kyauta ga dukkanin mutanen yankin a taron da aka yi a watan Janairun daya gabata.