An kafa cibiyar kula da tubabbun Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya, a yunkurin cimma burin kawar da ta'addanci a arewa maso gabashin kasar da gwamnatin tarayya ta yi alkawarin yi, da kuma kokarin neman lafiya da gyara halayyan 'yan kungiyar da suka mika wuya, ma'aikatar tsaron kasar ta kafa wata cibiyar kula da ire-irensu, wadda ta kira Operation Safe Corridor.

Dalilin kirkiro wannan cibiyar ta Operation Safe Corridor shi ne domin sake ilmantar da kuma shigar da tsoffin 'yan ta'addan cikin al'umma, domin su sauya rayuwa mai inganci.

Cibiyar ta 'yan ta'adda da suka mika wuya, za ta koya masu sana'o'i kala-kala ta yadda al'umma da ma tattalin arzikin kasar zasu amfana dasu.

Ma'aikatar tsaron tayi kira ga sauran 'yan kungiyoyin da har yanzu ke ayyukan ta'addanci ga al'umman da basu ji ba basu gani ba, da su ma su mika wuya domin samun gatan da wannan cibiyar ke samarwa.