An zargi Sojojin Congo da lalata

Majalisar dinkin duniya ta ce ta karbi korafin zarge-zargen cin zarafi ta hanyar yin lalata, da dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Tanzaniya suka yi a gabashin jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce 11 daga cikin dakarun suna fuskantar tuhuma, ta yarda da zama iyayen wasu da aka haifa, sannan akwai shaida da ke nuna wasu daga cikin dakarun, sun yi lalata da kananan yara.

A wani bangaren kuma, wasu sojojin Congon suna fuskantar shari'a a Kinshasa babban birnin kasar bisa zargin su da cin zarafi ta hanyar lalata a kasar jamhuriyar tsakiyar Afirka.

Su ne sojoji na farko da suka fuskanci shari'a, a babbar badakalar cin zarafi ta hanyar lalata da ake zargin sojojin Faransa da dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a jamhuriyar Tsakiyar Afirka.