Nigeria: Ƙarancin mai ya yi ƙamari a Bauchi

Image caption Layin 'yan babura a gidan mai a Bauchi.

A birnin Bauchi da ke Najeriya, dubban mutane ne ke yin dandazo a gidajen man fetur, ƙalilan ɗin da ke sayar da man.

Rahotanni na cewa wasu ma kan kwana a kan layi.

Farashin dai a wasu wurare ya ninka farashin da gwamanti ta ƙayyade na naira 87 kan kowace lita har sau uku.

Kusan dukkannnin manyan biranen kasar suna fusknatar wannan matsala.

Nijeriya dai ta daɗe tana fama da matsalar ƙarancin man fetur duk da cewa tana ɗaya daga cikin ƙasashen duniya mafiya arziƙin man fetur.

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Wasu matasa na amfani da injin jannareta wajen samun mai.

Sai dai kuma wasu rahotanni na cewa matasa na amfani da matsalar wajen arzurta kansu.