Zamu dauki mataki kan Masar -Italiya

Hakkin mallakar hoto epa

Italiya ta yi barazanar daukan mataki na ramuwa dai-dai gwargwado, kan mutuwar da wani dalibi dan italiya ya yi a Masar, muddin Masar din bata bada hadin kai wajen gano gaskiyar lamarin ba.

Giulio Regeni, dalibi ne mai karatu a matakin digiri ta uku a jami'ar Cambridge, wanda yake gudanar da bincike kan ayyukan kungiyoyin ma'aikata a Masar.

Dalibin ya bace a lokacin da ake tunawa da cika shekaru 5 da juyin-juya halin kasar, sannan bayan kwanaki 9, aka gano gawarshi a wani rami.

Ministan harkokin wajen Italia ya shaidawa Majalisar dokokin kasar cewa kasar za ta dauki mataki, har sai masar din ta sauya take-takenta game da binciken da ake gudanarwa.