Libya: 'Yan tawaye sun miƙa wuya

Sabuwar gwamnatin Libya

Asalin hoton, epa

Bayanan hoto,

Sabuwar gwamnatin Libya

'Yan tawayen Libya dake ikirarin shugabancin kasar a birnin Tripoli sun mika iko ga gwamnatin dake da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya

An bayyana matakin ne a wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizon ma'aikatar shari'ar kasar.

Sanarwa a madadin gwamnatin 'yan tawayen mai kiran kan ta gwamnatin ceton kasa ta ce, ta sauka ne a bisa bukatun 'yan kasar da kuma kaucewa zub da jini.

Hakan na zuwa ne mako guda bayan da sabon Pira ministan gwamnatin hadin kan kasar Fayez al-Sarraj ya isa birnin Tripoli.

Sabuwar gwamnatin Libyar ta tare a Tripoli babban birnin kasar ne a makon jiya da nufin karbe ikon kasar, kuma tun a wannna lokacin tana gudanar da al'amuranta a wani sansanin sojin ruwa.

Har yanzu dai kasar ta Libya na da hukumoni daban-daban da basa ga maciji da juna dake zaune a gabashin kasar da kuma Tripoli babban birnin kasar.

Wannan gwamnatin wacce kasashen duniya ba su amince da ita ba, ta rike mulkin ne tun a shekara ta 2014, bayan wata arangama tsakanin kungiyoyin masu rike da makamai a birnin Tripoli, da ya tilsatawa zababbiyar gwamnatin tserewa zuwa gabasghin kasar.

Matakin baya-bayan nan zai bayar da dama ga sabuwar gwamnatin hadin kan da ke da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya rike ragamar ikon kasar da ke fama da rarrabuwar shugabanci.