US: Za a takawa 'yan luwadi birki

'Yan luwadi da madigo a Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan luwadi da madigo a Amurka

Gwamnan jihar Mississippi ta Amurka ya amince ta dokar da za ta baiwa kamfanoni, da kungiyoyi damar takawa ma'aurata 'yan luwadi birki.

Dokar zata basu damar kin yin wata mu'amala da ma'auratan jinsi daya, muddin abinda suka aikata ya saba da addininsu.

Gwamnan Phil Bryant wanda dan jam'iyar Republican ne, ya rattaba hannu kan dokar duk kuwa da adawar da wasu kungiyoyi ke yi da ita a kan cewa zata haifar da nuna wariya.

Gwamanan jihar New York State, Andrew Cuomo, ya haramta duk wani bulaguro da ba wani muhimmi ba zuwa jihar ta Mississippi sakamakon wannan sabuwar doka.

Kungiyar kare hakkin biladama ta Amurka (ACLU) ta ce, dokar ta saba wa duk wasu hukunce-hukuncen Amurka na yin adalci da kuma daidato ga al'umma.

Gwamna Bryant, dai ya ce ya rattaba hannu a dokar ne don kare martabar addinai da kuma yanayin da'ar wasu al'ummomi, da kamfanoni masu zaman kansu da ma ungiyoyi, kan abinda ya kira matakin nuna wariya daga gwamnati.