Aung San Suu Kyi na neman Ofishin Firayi Minista

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Aung San Suu Kyi ce ta yi nasara lashe zaben shugaban kasar, amma wata doka ta kasar ta hana duk wanda ke da dangantaka a kasashen waje, zamowa shugaban kasa.

Majalisar dokokin Myanmar ta amince da wani kuduri na samar da sabon mukamin mai bayar da shawara ga kasar, da za a bai wa jagorar masu rajin kafa dimukradiyya, Aung San Suu Kyi.

Muhimmancin mukamin, kwatankwacin ofishin Firayi minista ne.

'Yan majalisar dokokin na bangaren soji, wadanda ba zaban su aka yi ba, sun kauracewa kada kuri'ar, tare da yin bore yayin da ake amincewa da kudurin.

Babu dai tasirin da boren ya yi, saboda a majalisar, 'yan jamiyyar Aung San Suu Kyi ne ke da rinyaje.

Yanzu, amincewar shugaban kasar, wanda na hannun damar Aung San Suu Kyi ne, kawai ake bukata ya mayar da kudurin doka.

Kundin tsarin mulkin kasar ya haramtawa Aung San Suu Kyi zama shugabar kasa, amma, ta sha nuna cewa, ita ce za ta zama kashin bayan kowace irin manufa da gwamnati za ta tsara.