Panama: Cameroon na fuskantar matsin lamba

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption David Cameroon tare da William Hague da George Osborn

Firaiministan Ingila, David Cameroon yana fuskantar matsin lamba dangane da takardun sirrin da kamfanin lauyoyi na Mossack Fonseca ya fitar, kan safarar kuɗaɗe da kin biyan haraji.

Takardun dai sun nuna cewa kamfanin ya yi wa kamfanonin fiye da 100,000 rijista a asirce, a tsuburran da ke kusa da Birtaniya.

Jagoran jam'iyyar adawa ta Labour, Jeremy Corbyn ya ce ya kamata gwamnati ta sanya ido kan gujewa haraji.

Sai dai kuma fadar gwamnatin Birtaniya ta mayar da martani cewa kasar ta wuce cuwa-cuwa a harkar biyan haraji.