Kamaru: An kama 'yan Boko Haram 300

Hakkin mallakar hoto AFP

Kwamandan dakarun rundunar hadin gwiwa na tabbatar da tsaro a yankin tafkin Chadi shiyya ta farko a Kamaru, ya tabbatar da cewa sun yi nasarar kama mayakan kungiyar Boko Haram kusan 300.

Kazalika, sun kuma aka kubutar da mutane sama da 2,000 da mayakan suka yi garkuwa da su.

Wannan nasara ta biyo bayan aikin hadin gwiwa da aka samu a tsakanin dakarun Najeriya da kuma Kamaru a garin Walassa da ke yankin arewa maso gabashin Najeriyar.

Ga rahoton da wakilinmu Muhamman Babalala ya hada mana:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti