Yawan masu ciwon suga ya karu a duniya

Image caption Ciwon suga cuta ce mai saurin kisa

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce yawan masu fama da ciwon suga, Diabetes, ya kai wani mataki da ya zarce na lokutan baya, inda yanzu ake samun daya cikin mutane 11 a fadin duniya dake fama da ciwon.

Hukumar ta WHO ta ce mutane miliyan 422 ne suka yi fama da ciwon suga a shekarar 2014, adadin da ya rubanya wadanda suke dauke da cutar a 1980 har sau hudu.

A rahotonta na farko kan masu fama da ciwon suga a duniya, hukumar ta WHO ta ce cutar ta Diabetes ce ta yi sanadin mutuwar mutane miliyan daya da rabi a shekarar 2012, kuma lamarin yana karuwa a kasashe masu tasowa.

Alkaluma na baya-bayan nan sun nuna cewa kasashen da ke yammacin Facifik, su suka fi yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon cutar ta diabetes.