Sunan jami'in FIFA ya fito a jerin Panama

Image caption Kamfanin Mossack ne ke kwarmata bayanai kan masu kadarori a tsibirin na Panama.

Wani babban jami'i a hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ya yi murabus daga kwamitin da'ar hukumar bayan da aka ambato sunansa a jerin badakalar boye kudi na tsibirin Panama.

Juan Pedro Damiani wanda lauya ne dan Paraguay ya taimaka wajen kafa kwamitin.

Takardun sirrin da aka kwarmata sun nuna cewa kamfaninsa ne ya yi aiki ga wasu kamfanoni bakwai da suke kasashen waje wadanda suke da alaka da tsohon mataimakin shugaban FIFA Eugenio Figueredo, wanda ke fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa a Amurka.

Kwamitin da'a na FIFA na binciken sanin ko an karya ka'idodinsa.

Mista Damiani ya yi watsi da zargin aikata duk wani mugun abu.