Wayar Huawei P9 na da kyamara mai mudubi biyu

Kamfanin wayar salula Huawei
Image caption Kamfanin wayar salula Huawei

Kamfanin Huawei mai kera wayar salula, ya kaddamar da sabuwar wayar komai da ruwanka samufurin da ke amfani da kyamara mai mudubi biyu.

Hakan zai taimaka wa masu amfani da ita su iya sake saita hotuna bayan sun dauka.

An yi wannan fasaha ne sakamakon hadin guiwa tsakanin kamfanin kere-kere na kasar China da kuma kamfanin Leica mai kera kyamarori na kasar Jamus.

Hakan na nufin samfurin wayar ta P9 za ta iya daukar hotunan da sai wayoyi masu babban madubi ne za su iya dauka.

Masu sharhi sun ce wannan sabuwar fasaha za ta taimaka wa kamfanin na Huawei matsayi da kuma bunkasa kasuwar hannayen jarinsa.

Kamfanin mai mazauni a birnin Shenzhen- ya fitar da wayoyin salula fiye da miliyan 106 zuwa kasashen waje a shekara ta 2015 kamar yadda wata hukumar bincike ta bayyana.

Hakan shi ne bunkasar ciniki mafi girma da kamfanin wayar na Huawei ya samu, da kuma ya saka shi a matsayi na uku cikin kamfanoni mafiya bunkasa a kasuwar hannayen jari.