Ana taron bunkasa tattalin arziki a Kaduna

A Najeriya, an bude wani taron kokarin habbaka tattalin arziki da sanya jari a jihar Kaduna.

Taron dai na tattaunawa ne da 'yan kasuwa masu saka jari na gida da na ketare domin bunkasa samar da ayyukan yi ga jama'a.

Tuni dai kamfanin Dangote ya ce zai saka jari na Dala miliyan Goma a Kaduna a matsayin gudunmawarsa ga bunkasa masana'antu a jihar.

A kwanan baya ma an bude wani taron koli na kwanaki biyu domin duba halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki gaba daya.

Taron wanda aka gudanar a babban birnin kasuwanci na kasar wato Legas, ya duba yadda duniya ke kallon tattalin arzikin Najeriya, da kuma hanyoyin zuba jari a kasar da ma yankin yammacin Afrika.

Matsalar rashin ayyukan yi ga matasa da karancin man fetur da wutan lantarki na cikin kalubalen da tattalin narzikin kasar ke fuskanta.