Kenya: An samu raguwar cutar Malariya

Hakkin mallakar hoto WELLCOME TRUST
Image caption Ana matukar fama da cutar ta Malariya a Afrika ta Yamma, inda kashi 30 cikin 100 na kananan yara ke dauke da ita.

Wani sabon bincike kan kiwon lafiya a Kenya ya nuna cewa an samu raguwar adadin mutanen kasar dake kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro, watau Malaria.

Wasu alkaluma daga ma'aikatar lafiya ta kasar sun nuna cewa kashi 8 cikin dari na mutane ne suka kamu da cutar a wannan shekarar, kasa da kashi 11 cikin dari da aka samu a shekarar 2010.

Binciken ya gano nasarar da aka samu a kan karuwar amfani da gidan sauro, da kuma yadda jama'a ke maganin cutar da wuri.

Sai dai har yanzu, cutar Malariya ce aka fi fama da ita a Afirka ta yamma, inda kashi 30 cikin dari na kananan yara ke dauke da ita.

Kimanin mutane dubu 500 ne suka mutu bara a duniya sakamakon cutar ta Malaria, kuma mutane tara cikin goma na wadanda suka mutun, a kasashen Afirka dake kudu da hamadar sahara suke.