Kamfanin tasi na Uber na fuskantar kalubale a Kenya

Kamfanin tasi na Uber
Image caption Kamfanin tasi na Uber

Kamfanin tasin da ke mu'amula ta intanet da ke aiki a wasu manyan kasashen da suka ci gaba wanda ake kira Uber ya fara shigowa Afrika

Kamfanin na Uber na bai wa mutane a manyan birane damar hawa motocin tasinsa a farashi mai sauki.

Sai dai a Nairobi babban birnin Kenya, direbobin tasi-tasi na birnin suna adawa da kamfanin, inda inda a 'yan watannin da suka gabata aka rika samun dauki-ba-dadi tsakanin bangarorin biyu, har sai da ta kai 'yan sanda da ma'aikatar sufuri suka shigo cikin lamarin.

To amma duk da haka wannan kamfani na ci gaba da bunkasa, inda aka kara fadada aikinsa zuwa birni na biyu mafi girma na kasar ta Kenya, wato Mombasa.