Shin ka san Sani Aliyu Ɗandawo kuwa?

Hakkin mallakar hoto Faruk Malami Yabo
Image caption Marigayi Sani Dandawo ya rasu da shekara fiye da 70

Sani Aliyu Ɗandawo, fitaccen mawaƙin sarauta ne a ƙasar Hausa.

A ranar Lahadi ne dai ya rasu, a garin Yawuri na jihar Kebbin Najeriya, yana da shekaru fiye da 70.

Wasu mawaƙa da maroƙa a arewacin Najeriya na nuna damuwa kan rasuwar fitaccen mawakin, wanda suka ce zai wuya a iya cike giɓin da ya bari.

Saurari Alhaji Umar Ɗan Ama, wani fitacce maroƙi a jihar Sakkwato kuma aminin marigayin na tsawon shekaru 20, yadda ya bayyana wa Haruna Shehu Tangaza, irin halayyar Sani Ɗandawo.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti