Za a miƙawa Buhari cikakken kasafin kuɗin 2016

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A watan Disamba ne Muhammadu Buhari ya kai kasafin kudin kasar gaban majalisar Najeriya.

A ranar Alhamis ne ake sa ran akawun Majalisar Dokokin Najeriya zai mika cikakken kudurin kasafin kudin kasar ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Tun a ranar Laraba ne dai shugabannin kwamitocin kasafin kudi na majalisar Dattawa da ta Wakilai suka rattaba hannu a kan kammalallen kasafin.

Makwanni biyu da suka wuce ne aka mika kudurin a takaice amma shugaban kasar ya ce ba zai sa hannu ba har sai ya ga cikakken bayani game da kasafin.

Majalisar dokokin Najeriyar ta zartar da kasafin kudin na kimanin dala biliyan 30 wanda ba a taba kasafi mai yawa irinsa ba, don farfado da tattalin arzikin kasar wanda ya tabarbare sakamakon faduwar farashin man fetur a duniya.