Sharhi kan zaben Chadi na 2016

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Deby na son yin tazarce karo na biyar

A ranar 10 ga watan Afrilu ne al'ummar kasar Chadi za su kada kuri'a domin zabar sabon shugaban kasa.

Shugaba mai ci Idris Deby dan shekara 64, yana son ya yi tazarce a karo na biyar inda zai fafata da 'yan takara 13 daga jam'iyyun adawa.

Hukumar kundin tsarin mulki ta Chadi ta dakatar da

Mutane miliyan 6.26 ne suka yi rijistar zabe daga cikin kiyasin al'ummar kasar miliyan 12.28. Tun bayan samun 'yancin kai da Chadi tayi daga Faransa a shekarar 1958, kasar ke fama da rikice-rikice.

Majalisar tsarin mulkin kasar ta haramtawa babban dan adawar Idris Deby tare da wasu 'yan takara guda biyar tsayawa takarar, a zaben da ake ganin za a yi gwagwarmaya.

Su waye 'yan takarar?

Idriss Deby Itno shi ne dan takarar jam'iyyar Patriotic Salvation Movement, wanda kuma yake kan karagar mulkin kasar tsawon shekaru 26. Ya dare kan mulkin ne bayan wani juyin mulkin soji da aka yi wa Hissene Habre a shekarar 1990, kuma a yanzu yana daga cikin shugabanni Afrika da suka dade a kan mulki.

An sake zabar shugaba Deby a shekarar 2011, inda 'yan adawa suka kauracewa zaben. Ya kankane duk wasu manyan al'amura na kasar. Deby ya kulla abota ta kut da kut da kasashen yamma wajen yaki da ayyukan ta'addanci a yankinsa.

Shugaban kungiyar ci gaban kasa da farfado da ita Saleh Kebzabo, ya tsaya takara har sau biyu don ganin ya yi nasara a kan Deby a shekarar 1996 da ta 2001, amma ko yaushe shi yake zuwa na uku. A shekarar 2006 da 2011 kuwa sai Kebzabo ya kauracewa zabukan.

Kebzabo wanda dan jarida ne, ya yi minista har sau biyu karkashin gwamnatin Deby tsakanin 1993 zuwa 2001 kafin daga bisani ya zama dan adawa.

Joseph Djimrangar Dadnadji kuwa ya yi Firai minista daga shekarar 2013 zuwa 2015 kafin ya yi murabus ya kuma kirkiro da jam'iyyar Popular Action Framework for Republican Solidarity and Unity.

Ya ya tsarin zaben yake?

Kundin tsarin mulki ya samar da tsarin samun sakamako mafi rinjaye a zagaye biyu. Dole ne dan takara ya samu kashi 50 cikin 100 da kuma samun nasarar a zagayen farko kafin ya lashe zaben.

Idan ba a samu bayyanannen wanda ya yi nasarar ba a zagaye na farko, dole 'yan takara biyu da suke da rinjaye a zagayen farkon za su fafata a zagaye na biyu.

Hukumar zabe ta kasa ce za ta gudanar da zaben karkashin sa idon ma'aikatar harkokin cikin gida. Ana kuma sa ran kungiyoyin sa ido kan zabuka na kasashen waje za su turo da wakilai.

Mene ne ainihin batutuwan?
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ayyuakan ta'addanci na daga cikin matsalolin da Chadi ke fuskanta

Duk da arzikin man fetur da kasar ke da shi, mafi yawan 'yan Chadi na rayuwa ne cikin talauci. Faduwar farashin man fetur a duniya da kuma ayyukan ta'addanci da ya gallabi yankin ya kara sa al'amarin talauci ya ta'azzara.

Rashin biyan albashin ma'aikata kan lokaci da kuma rashin daukar ma'aikata akai-akai ya janyo zanga-zangar adawada shugaba Deby cikin watanni uku da suka gabata.

'Yan adawa dai na ganin saukar Deby daga mulki ne kawai mafita.

Yaya batun kamfe?
Image caption An yi zanga-zangar hura usur don nuna adawa da shugaba Deby

A watan Fabrairu ne aka yi wa diyar dan takarar shugabancin kasa Mahamat Brahim Ali fyade, al'amarin da ya jawo zanga-zangar bacin rai da har Deby ya kori ministocinsa daga aiki.

Tsawaita wa'adin da aka diba na haramta zanga-zanga a watan Maris ya kara jawo wani tashin hankalin, wanda ya hada da tafiya yajin aikin sai baba ta gani inda al'amuran kasar suka tsaya cak.

Dakarin tsaro kuma sun kama masu fafutuka na bangaren adawa domin shirya wata zanga-zanga da masu yinta suka dinga hura usur don neman Deby ya sauka daga mulki.

Dan takarar jam'iyyar adawa Kebzabo ya I gargadi cewa mutanen Chadi suna fuskantar babban tashin hankali gabannin zabe.

Wa ake ganin zai yi nasara, kuma me yasa?

Ana ganin dai Deby yana da karfin lashe zaben nan kuma zai zama shugaba a karo na biyar, duk kuwa da cewa ana tababar ko za a yi sahihin zabe. A kowanne lokaci aka yi zagaye na farko na zabe shi yake lashewa sai zaben da aka yi a shekarar 1996 ne kawai aka samu akasi.

Kazalika, har yanzu 'yan adawa suna da yakinin za su iya lashe zabe, musamman idan aka je zagaye na biyu na zaben.

Bayanai: Sashen bincike na BBC