Brussels: Ana farautar mai malafa

Hakkin mallakar hoto Belgian Police

Masu shigar da kara a Belgium sun sake yin roko na neman taimako a farautar da suke ta mutumin da ke sanye da malafa, wanda aka gani a hoton bidiyon tsaron filin jirgin sama na Brussels da ake zargi da kai harin watan jiya.

An gan shi tare da 'yan kunar bakin waken biyu, sannan kuma bayan tashin bama-baman an gan shi yana gudu a cikin mutane yana kokarin tserewa daga wajen.

Wakilin BBC ya ce yanzu mahukuntan sun fid da wani sabon hoton bidiyo na kyamarar tsaro (CCTV) da kuma wasu hotuna yayin da yake barin filin jirgin saman.

Wasu hotunan kuma sun nuna shi yana tafiya a tsakiyar birnin Brussels, yana magana a waya.

An yi kira ga mazauna birnin da su fito da duk wasu karin hotunan mutumin da ka iya taimakawa a gano shi.

A kwanan baya ne bama-bamai guda biyu suka fashe a filin jirgin sama na Zaventem da ke birnin Brussels, a Belgium, inda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 31, da jikkata mutane da dama.