Lugudan labba tsakanin manyan Malaman Iran

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Iraniyawa sun samu batun tattaunawa na sabanin da ke tsakanin Malaman kasar

A yayin da Iraniyawa ke komawa bakin aiki a wannan makon bayan hutun sabuwar shekara da suka yi, maganar da za a fi yi ita ce batun mummunar barakar da ta kunno kai tsakanin manyan malaman addini na kasar.

Mutane sun saba ganin rikici tsakanin masu sassaukan da masu tsattsauran ra'ayi, da kuma tashin hankali tsakanin zababbun shugabannin kasa masu kokarin kawo sauye-sauye da kuma masu tsaurin ra'ayi da basa maraba da sauyi.

Amma a mmakon da ya gabata wata gaba ta kunno kai tsakanin manyan mutanen kasar da suka hada da jagoran addini Ayatollah Khamenei da kuma tsohon shugaban kasar Ali Akbar Hashemi Rafsanjani, wanda a da suke kut-da-kut amma a yanzu sun zama abokan gabar juna.

Wannan rigima ce da ke kawo shakku a zuciyar mutane kan wacce irin kasa Iran za ta zamo nan da shekaru masu zuwa.

"Ma zai faru a gaba"
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kalaman Mista Rafsanjani ne suka fara hura wutar babatun

Sa'insar ta fara ne da wani sako a shafin twitter da aka rubuta daga wani shafi mai alaka da Mista Rafsanjani a makon da ya gabata, inda yake kira da cewa kamata ya yi a hau teburin tattaunawa da kasashen duniya maimakon lugudan labba.

Abin da sakon ke cewa dai shi ne, "Duniyar gobe ta sasantawa ce ba ta aika makamai masu linzami ba."

Mista Rafsanjani wanda ke jagorantar majalisar koli ta addini wadda ke da fada a ji, babban na hannun damar shugaba Hassan Rouhani ne.

Nasarar da wadannan mutane da kuma magoya bayansu suka samu a baya-bayan nan a zabukan kasar da aka yi, ya bai wa Mista Rafsanjani damar samun babban matsayi inda kuma yake amfani da wannan damar wajen sukar masu tsattsauran ra'ayin addini.

Kazalika, sakon Mista Rafsanjani na twitter ya nuna irin yadda ya kai matuka a sukar wancan bangaren, al'amariin da ya kara fusata su.

Shi kuwa Mista Khamenei cewa ya yi, "Duk masu cewa cigaban Iran ya ta'allaka ne kan sasantawa ba aika makami mai linzami ba to sun yi kuskure."

Ya kara da cewa duk dan Iran din da ya fadi haka, to jahili ne ko kuma butulu.

Wannan batu na Mista Khamenei ne limamai suka dauka suka kuma dinga amfani da shi a hudubar Juma'a a masallatai.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masallatan kasar sun mayar da batun abin yin hudubar Juma'a

A masallatan kasar dai limamai sun yi watsi da amfani da kalaman yaudara, suka kuma ce za a kori duk mai yada su daga aiki.

Basu dai ambaci sunan Rafsanjani ba, amma kowa ya fahimci cewa shi ake nufi da wannan kalamai.

'Sa'insar cikin gida'

a wasu kasashen irin wannan mayar da martani na nuna alamar cewa wani jami'i na iya rasa aikinsa da ma darajarsa, amma a Iran abubuwa ba haka suke ba.

Sabani tsakanin manyan jami'ai wani abu ne da ya zama tamkar al'adar kasar.

Ana ganin hakan a wani al'amari na rikicin cikin gida, wanda ake iya jurewa har na tsawon lokaci.

Wani babban misali mai kyau shi ne jagoran addini Ayatollah Khamenei da kansa. Akwai matukar sabani tsakaninsa da wanda ya kirkiri daular Musulunci ta Iran wato Ayatollah Khomeini, a lokacin da shi Mista Khamenei yake shugabantar kasar a shekarun 1980.

Hakkin mallakar hoto khamenei.ir
Image caption A can baya shima Mista Khamenei ya samu sabani da Ayatollah Khomaini na wancan lokacin

Irin wannan sa'insa dai na faruwa ne idan ana ganin cewa mutum baya daga cikin wannan bangare.

Alal misali, Mir Hossein Mousavi shi ne tsohon Firai ministan kasar kuma dan cikin gida, amma ya shafe shekaru biyar ana masa daurin talala bayan da ya zama dan adawar Mahmoud Ahmadinejad a zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekarar 2009 mai cike da rudani.

Mista Rafsanjani na daga cikin manyan 'yan siyasar da za a ambata a kasar, amma wata alama da ke nuna cewa wannan sa'insar ta hanashi sakat shi ne yadda ya janye kalaman da ya yi a shafin twitter tun farko, wadanda suka jawo wannan lugudan labba.