"Yadda nake fama da talauci"

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army

Wasu 'yan Najeriya masu ƙaramin-ƙarfi na kuka da matsin tattalin arziƙin da ƙasar ta tsinci kanta a ciki, sakamakon raguwar kuɗin-shigar gwamnati, wadda faduwar farashin mai ta haddasa, da kuma wasu matakai da mahukunta suka dauka na yaƙi da cin hanci da rashawa.

Masu ƙaramin ƙarfi mazauna birane da yankunan karkara na cewa matsi ya yi matsi, suna fata gwamnatin ƙasar za ta hanzarta wajen yassare musu wahalarsu.

Ibrahim Isa ya ziyarci gidan wani mara galihu a garin Gimare da ke jihar Nasarawa a tsakiyar Najeriyar don ganin yadda iyalansa ke gudanar da rayuwarsu, ga kuma rahoton da ya aiko mana.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti