Nigeria: Gwamnati za ta tallafa wa marasa galihu

A Najeriya mataimakin shugaban ƙasar, Yemi Osinbajo, ya ce, gwamnati na shirin bayar da tallafi na kuɗi na kusan dala 25 ga al'ummar ƙasar marasa galihu,a duk wata, domin rage matsanancin talaucin da suke fama da shi.

Ranar Alhamis ne Mr Osinbajo ya bayyana haka, inda ya ƙara da cewar wannan shiri zai buƙaci kuɗi dala dubu 300 daga lalitar gwamnati a duk shekara.

A watan Maris ɗin shekarar 2015, lokacin yaƙin neman zaɓe, shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa al'ummar ƙasar alkawarin yaƙi da talauci da cin hanci da rashawa da mutane miliyan 180 na ƙasar ke fama da shi, duk da arzikin man fetur da ƙasar ke taƙama da shi.

Sanarwar da mataimakin shugaban ƙasar ya fitar wadda ta zayyana shirye-shiryen da ya ce, gwamnati za ta sanya a gaba nan da watanni 12 nan gaba,

Ya ce, "Mutane miliyan ɗaya dake cikin matsanancin takura da talauci, za a bai wa naira 5000 duk wata (watau dala 25)."

Ya ƙara da cewa, gwamnatin Najeriyar na shirin daukar matasa dubu 500 da suka kammala karatu aikin Malaman makaranta, kafin su samu ayyuka na son ransu.

Mr Osinbajo dai bai bayar da bayanin ta yarda gwamnati za ta dauki nauyin wadannan shirye-shirye ba, inda ya bayar da tabbacin tsarin na cikin kasafin kudin naira fiye da tiriliyan 6 da majalisar ƙasar ta amince da shi, duk da cewar shugaba Buhari bai sanya hannu ba tukunna.

Gwamnatin shugaba Buharin dai na fuskantar kalubale a 'yan makwannin nan, game da batutuwan karancin man fetur , da ma faduwar da farashin man ya yi a kasuwanni duniya wadanda ke janyo wa tattalin arzikin kasar koma baya.