An mika wa Buhari cikakken bayanin kasafin kudi

Image caption Kawu Sumaila ya shaida wa BBC cewa sun karbi cikakkun bayanan kasafin daga Majalisa

<span >Majalisar dokokin Nigeria ta mika cikakkun bayanan kasafin kudin kasar ga fadar shugaban kasa domin sanya hannu.

Abdurrahman Kawu Sumaila mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin majalisar wakilai, ya shaida wa BBC cewa, sun karbi kasafin kudin, kuma sun mika shi ga shugaban kasa.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari dai ya sha alwashin sai ya bi kasafin kudin dalla-dalla kafin ya sa masa hannu.

Makwanni biyu da suka wuce ne aka mika takaitaccen kudurin amma shugaban kasar ya ce ba zai sa hannu ba har sai ya ga cikakken bayani game da kasafin.

Majalisar dokokin Najeriyar ta zartar da kasafin kudin na kimanin dala biliyan 30 wanda ba a taba kasafi mai yawa irinsa ba.