Sudan Ta Kudu: Riek Machar na shirin komawa gida

Hakkin mallakar hoto Getty

Jagoran 'yan tawaye na Sudan ta Kudu, Riek Machar ya ce ran 18 ga watan Apirilu ne zai koma gida daga gudun hijirar da yake.

A watan Desembar shekara ta 2013 lokacin da aka fara yakin basasar kasar ya gudu kuma tun lokacin ya ke zaune a Habasha.

Komawarsa gida zata zama mai muhimmanci saboda lokacin ne za'a kafa wata gwamnatin hadin kan kasa.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma a watan Agusta, Mr Machar ne zai zama mataimakin shugaban kasa na daya.

Dubban mutane ne dai aka kashe tun lokacin da aka fara yakin basasar, kuma sama da mutane miliyan biyu sun rasa