Karancin mai a kasar da tafi arzikin man fetur a Afrika

Ya ya kasar da tafi kowacce arzikin mai a Afrika take fuskantar karancin man fetur?

Duk da cewa Nigeria ce kasar da tafi kowacce arzikin man fetur a duniya, hakan bai hanata shigo da tataccen man fetur din da ake amfani da shi ba. Bata da isassun matatun man fetur.

Wani masanin tattalin arziki John Ashbourneo ya ce, ko da ace matatun man da kasar take da su guda hudu na aiki yadda ya kamata, to ba za su iya samar da kashi daya bisa hudu ne kawai na yawan man da ake bukata.

Idan ana son samar da isasshen abin da kasar ke bukata, to dole kamfanin man fetur na kasar ya dinga shigo da kashi 50 cikin 100 na man fetur din da ake bukata> sauran kashi 50 din kuwa 'yan aksuwa masu zaman kansu ne ya kamata su dinga shigo da shi.

Amma a tsawon watannin da suka gabata wadannan kamfanoni sun rage yawan man da suke shigo dashi, wanda hakan ya jawo karancin man fetur a kasar.

To me yasa?

1) Bashin da ba a biya ba

Shekaru, gwamnatin Najeriya na biyan wasu kudade a matsayin tallafin mai domin a sayar da shi da sauki ga 'yan kasa. Amma sai dai hakan ya yi matukar tsada sakamakon tashin farashin man a kasuwannin duniya.

Gwamnati mai ci yanzu ta ce ta tarar da dumbin bashi da ake bin tsohuwar gwamnati. An bar dillalan man fetur hannu wayam ba tare da biyansu kudadensu ba.

A karshe dai gwamnati ta biya bashin kudaden a watan Nuwambar 2015. Amma a wannan lokacin tuni kamfanonin suka fara rage shigo da man fetur din.

2) Tabarbarewar tattalin arziki
Hakkin mallakar hoto

Faduwar farashin man fetur na yin illa kwarai ga tattalin arzikin Najeriya. Hakan ya sa an samu raguwar dalolin Amurka da ake bukata don biyan masu shigo da mai.

Sun ce hakan ya tilasta musu amfani da kasuwar bumburutu inda suke biya da matukar tsada.

3) Rikicin biyan rarar man fetur

A watan Janairun 2016 ne gwamnati ta kawo karshen biyan tallafin man fetur da take yi a hukumance, tana mai cewa farashin man fetur ya fadi warwas ta yadda a yanzu ba a bukatar tallafin man.

Amma sai dillalan man fetur din suka ki yarda da wannan batu. Don nuna adawa da hakan ne ma wasu kamfanonin suka dakatar da sayar da man fetur din.

Yayin da karancin man ke kara kamari, sai wasu kuwa suka kara farashin nasu fiye da yadda gwamnati ta ce a sayar, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce.

Wasu masu sharhi dai sun yi hasashen cewa in har ba a dawo da biyan tallafin ba, to farashin da gwamnati ta ce a sayar da man zai sake karuwa, kuma dillalan man za su rage shigo da shi.

Ga 'yan Najeriya masu ababen hawa kuwa, hakan na nufin babu ranar da dogayen layukan da suka faman bi a gidajen mai za su ragu.