Volvo za ta gwajin motoci marasa direba

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kamfanin kera motoci samfarin Volvo na shirin gwajin motoci 100 da basu da direba.

Gwajin wadannan motoci samfanin volvo zai gudana ne a kasar Sin kamar yadda aka sanar.

Sai dai kuma ba a sanar da ranar da wanan gwajin zai gudana ba.

Kamfanin na volvo dai shi ne zai sanar da ranar da kuma garin da wanan gwajin zai gudana.

An yi ittifakin cewa, motocin da ke tuka kansu na taimakawa game da rage hadura a kan hanyoyi, kamar yadda Hakan Samuelsson shugaban gudanarwa na kamfanin Volvo ya sanar.

Shugaban kamfanin ya kara da cewa da zarar motocin sun fara aiki, to za su ceto rayuwar mutane da dama daga salwanta hadari.