Arsene Wenger ya yi korafi kan Jack Wilshere

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsene Wenger kocin Arsenal

Kocin Arsenal Arsene Wenger, ya yi wa dan wasan tsakiya Jack Wilshere fada a kan wani hotonsa da aka dauka ya fita yawo a daren ranar Lahadin da ta gabata.

Kwanan nan Wilshere mai shekaru 24 ya dawo daga horo amma kuma bai yi wasa ba wannan kakar sakamakon karayar da ya samu a kafarsa.

Arsene Wenger ya ce "Na yi masa magana kan abin da ya yi, sai dai an yayata maganar fiye da yadda take."

Kocin ya ce, "Mun fi so mu bar irin wadannan batutuwan a cikin gida."

Wilshere, dan wasan tsakiya na Ingila zai buga wasan 'yan kasa da shekara 21 a ranar Juma'a, a yayin da yake kara samun sauki bayan karayar da ya samu a kafarsa ta hagu a watan Agustan shekarar 2015.