An kammala yakin neman zabe a Chadi

'Yan takarar shugabancin kasa a Chadi sun kammala yakin neman zabe a ranar Juma'a.

Shugaba Idriss Deby tare da wasu 'yan takara 13 za su fatata ranar Lahadi domin fidda gwani.

Jam'iyyun siyasa 103 ne suka kulla kawance da MPS mai mulki.

A yayin da kowane dan adawa zai tsaya wa kanshi a zagayen farko na zaben.

Amma kuma bukatar 'yan adawar baki daya ita ce a samu kai wa zagaye na biyu domin su yi wa shugaban kasa taron dangi.

Ita kuma jam'iyar MPS mai mulki burinta shine ta lashe zaben a zagaye na farko.