An gurfanar da wasu 'yan fim a kotu

Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano, ta gurfanar da wasu masu harkar fim din Hausa su biyu a gaban wata kotu a jihar, bisa sayar da wani fim da ke kunshe da kalamai na rashi sanin ya kamata.

Hukumar ta gurfanar da Nuhu Abdullahi, wanda shi ne ya dauki nauyin fim din mai taken "Ana wata ga wata," da kuma Sani Abubakar wanda aka fi sani da Ram, a matsayin mutanen da ake zarginsu da yada fim din a jihar Kano, bayan hukumar ba ta amince da sakarsa ba.

Hukumar tace fina-finai dai ta tsaya tsayin daka cewa bata amince da fim din ba.

Mallam Ismail Na'Abba Afakallah wanda ke shugabantar hukumar tace finai-finai ta Kano ya ce "Fim din na dauke da maganganu da suke nuna rashin mutuntaka.

Ya kara da cewar hukumar ba za ta amince da yada irin wadannan fina-finai ba a al'umma, inda ya kara da cewa hakan bai dace ba.

Wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana da karin bayani daga Kanon.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti