An kori shugaban NFA Pinnick

Wata babbar kotu da ke jihar Plateau a Nigeria, ta kori shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Amoju Pinnick.

Hukumar ta kuma bayar da umarnin cewa Ambasada Chris Giwa ya dawo matsayin shugaba.

A ranar Juma'a ne kotun ta soke zaben da ya bai wa Pinnick damar darewa shugabancin hukumar da kuma wasu mambobin hukumar kwallon kafar.

A yanzu kotun ta yanke hukunci inda ta bai wa bangaren Giwa gaskiya kuma ta umurci gwamnatin tarayya ta dauke shi a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya.

Sai dai Pinnick ya yi watsi da bukatar ya sauka daga kan kujerar inda ya bayyana hukunci da cewa bai zama lallai ba.

Ya zuwa yanzu dai, hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, bata mayar da martani ba kan wannan batu.

Sai dai hukumar FIFA na adawa da kai kara a kan abubuwan da suka shafi kwallon kafa kotun farar hula.

Sani Fema wanda yana daya daga cikin 'ya'yan hukumar zartarwa na hukumar kwallon kafa ta Najeriya masu bin bayan giwa, ya shaida wa BBC cewa za su rushe duk abinda hukumar ta aiwatar karkashin jagorancin Pinnick.

Sani ya ce daya daga cikin matakan da za su rusa shi ne dawo da Stephen Keshi a matsayin kociyan tawagar kwallon kafa ta kasar.