South Africa: Dan zuma ya yi murabus

Image caption Duduzane Zuma(daga hannun dama) ya ce an yi masa muggan zato ga aikin sa tare da gidan Gupta.

Dan shugaban Afrika Ta Kudu, Jacob Zuma, ya yi murabus daga wani kamfani mallakin iyalan babban gida na Gupta, wadanda ake zargi da shisshigi a mulkin kasar.

Duduzane Zuma mai shekaru 33 ya yi murabus daga mukamin sa na Darakta a ma'aikatar ta Shiva Uranium ne bayan ya sha sukar siyasa.

Mataimakin ministan kudi Micebisi Jonas ya yi zargin cewa iyalan babban gidan na Gupta, sun yi karfi da yawa, inda a cewarsa, har shi suka yi wa tayin aikin Ministan kudi, kafin shugaba Zuma ya sauke wanda ke kan kujerar a watan Disamba da ya gabata, duk da cewar gidan Guptan sun musanta zargin.

Kamfanonin kudi da dama sun yanke mu'amala da kamfanonin iyalan na Gupta, bisa jita-jitan alakar gidan da shugaba Jacob Zuma.