Zaben kananan hukumomi na Abuja

Jami'in zabe  a Najeriya Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Jami'in zabe na dubu akwatunan zabe

An soma zaben kananan hukumomi da ke birnin tarayya Abuja.

Masu kada kuri'a zasu zabi shugabannin kananan hukumomi 6 da kuma kansiloli 62.

Sai dai bayannai sun ce masu zabe kalilan ne suka fito a rumfunan zabe.

Hukumar zabe ta ce ta yiwa masu zabe sama da miliyan daya rajista kuma sama da dubu 600 daga ciki sun karbi kartin rajistar zabensu.

Hukumar 'yan sanda ta ce ta tsaurara matakan tsaro a sassa daban - daban da ke fadin birnin domin tabbatar da cewa zaben ya gudana lami lafiya.